How To
Trending

Abinda Ya Kamata Kusani Lokacin Siyan Computer

Idan har ka tashi siyan computer yana da kyau ka duba computer mai kyau kuma wacce kakesa ran zatayi maka duk wasu abinda kake buqata, ni dai a shawara ta idan har kanason siyan computer don fara koyonta to kasiya computer mai wannan specification din;
Processor: Corei3
Processor Speed: 2:30ghz zuwa sama
RAM: 4GB
Screen Inch: Daga 13.5 zuwa 16
Hard Drive: Akalla 250GB zuwa sama
Kar ka damu da window operating system din da computer din zato zo dashi misali 64 bit ko 32bit domin wannan za a iya canjashi sannan brand din zaka iya zaban Hp, Dell, acer ko samsung amma nidai nafi amfani da Hp domin suna da kwari da kuma battery capacity. Computer mai wannan specifications din zakaji dadin amfani da ita domin kusan duk wani abu zaka yi dasu ko da kana dan koyo zaka cigaba da amfani dasu a gaba.
Sanna idan ka siya domin kare computer dinka daga virus attack shine ka nemi genuine and authentic antivirus ka sakawa computer dinka misali avast ko smadav sannan ka kula da irin softwares din da zakayi downloading ko zakayi installing da kuma irin website din da zaka ringa shig tare da kuma sannin wanne irin flash ko hard drive zaka ringa sakawa a jikin computer din. Don haka bayan Sadiq akwai mutane da yawa misalin a nan facebook, youtube, instagram da kuma tiktok da zaka iya dubawa ko ka bibiya domin samun ilimin computer din nagode.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Click Here To Enjoy Free Browsing