Graphics Design
Trending

Abubuwan Kula Idan Kuna Son Zama Graphic Designers

Bafa samun kayan aiki ko software din graphic design ke nuna cewa mutum ya zama graphic designer ba. Kafin mutum ya zama graphic designer har ya kai ya zama professional akwai abubuwa da yawa da ya kamata mutum ya sani, a duniya bana tunani akwai abinda ake fara shi ko akeyin shi haka kawai ba tare da an tsara shi ba, shima haka graphic design yake ilimi ne babba mai zaman kansa.

A matsayin wanda kakeson zama graphic designer abinda ya kamata ka sani shine ba samun kayan aikin ba, akwai fundamental ilimin shi kanshi graphic design din daga cikin su kuwa sun hada da;
1) Concept: Abinda nake nufi da hakan shine tsarin ma ya zakayi shi kanshi design din naka ya kakeson ka aiwatar dashi yadda zakayi haka kuwa yana kyau ka fara sketching ko da rough ne a takarda kafin ka fara aikin sa, wani lokaci kafin ka fitar da design daya sai kayi kusan akalla guda 5-10

2) Typography; Typography shine tsarin arrangement na rubutu, shape da clips art a cikin design, ba haka kawai ake design ba, ba tare da tsara inda zaka ajiye kowanne rubutu, shapes ko clips art a muhalinsa ba.

3) Fonts; wato rubutu kenan shi kanshi font kamar magana ce ko sako da kakeson isarwa a cikin design kowanne font akwai amfanin sa akwai kuma inda ya dace a sakashi a cikin design akwai fonts kala-kala kowanne category na rayuwa yana da irin nasa font din misali idan design zakayi na bakery ko abinda ya shafi abinchi akwai fonts wanda suka shafi wannan fannin zaku iya duba dafont, 1001 fonts fontsquirrel website, domin kuga ire-iren fonts da ake dasu har kuyi downloading free domin amfani dasu.

4)Color Managing; Saita kala kenan wannan shima na daya daga cikin muhimman abubuwa da graphic designer akeso ya mayar da hankali a kansu kowacce color ta na kiran wani abin akwai design din da warning ne ko danger kunga red color tana iya hawa akwai warm color da sauransu, a design kowacce color tana dauka wani abun da take nufi kuma akwae color combination din ba’a hadasu musamman mata ma sunfi maza sanin irin wannan.

Wannan sune kadan daga cikin muhimman abubuwan da akeson graphic designer ya sani kuma ya ringa amfani dasu wanda ina ganin zasu taimaka sosai, nima har yau ban kwarewa nayi ba duk design din da nayi kafin na fito dashi ina turawa mentors su duba min inda nake da mistake a gyara mun, don haka bawai nayi rubutun nan ne don inyi discouraging kowa ba kawai dai ina bada shawarar ne na abinda ya dace, yana da kyau mutum ya samu mentor wanda zai ringa guiding nasa a koda yaushe hakan yana da kyau sosai. Nagode

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Click Here To Enjoy Free Browsing