How To
Trending

Bayani Akan Facebook Professional Mode

A shekarar da ta wuce  facebook sunyi updating features ta inda a yanzu suna bawa wasu profiles dama su mayar da profile dinsu kamar page, kamar yadda kamfanin meta suka sanar cewa wannan tsarin zai bada dama mutum ya ringa samun kudi ta hanyar hakan.
Sai dai mutane da yawa suna ta mayar da profile dinsu zuwa professional mode din amma tsarin ba na kowa bane kamar yadda meta suka sanar cewa tsarin zaiyi aiki ne ga content creators ( wato masu kirkira kenan), idan kuka kula tun a baya akwai sabon features da kamfanin meta suka kawo a cikin facebook wato REELS.

Reels features ne da aka saka a facebook da instagram kamar irin SHORTS na Youtube, tsari ne da ake bawa damar duk wani facebook user yayi posting videos na tsawon 30 to 60 seconds a cikin profile dinshi, wasu lokutan zaku dinga ganin wasu shorts videos da creators suke posting a reel na profile dinsu irin videos din sun hada da comedy, Tutorials, How To da sauransu. Irin wadannan creators din sune akayi professional mode don su, ta yadda facebook zai ringa saka talla a videos dinsu suna samun kudi ana biyansu kamar yadda dai akeyi a Youtube.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Click Here To Enjoy Free Browsing