How To

Google Form

Bayani Akan Google Form Tare Da Amfaninsa

Google form na daya daga cikin services din da kamfanin google suka samar domin saukakawa mutane wajen tare bayanai wanda suka shafi record na mutane, maki na exam ko kuma yin exam din ma ita kanta.

Abinda nake nufi shine amfani da google form na saukakawa wajen tattara bayanai, misali idan kai malamin makaranta ne ko kuma dan kasuwa ko kuma kana aikin da ya shafi ajiye record na mutane wato samun bayanansu ta hanyar basu form su cike, to a yanzu google sun taimaka maka ba sai ka sha wahalar yin printing form physically kana rabawa mutane ba, a yanzu kawai zaka iya creating form ne online ka turawa mutane su cike kai kuma kana ajiye record din, kai da kanka zaka saka tambayoyin da kakeson mutane su cike da kansu ba sai kun hadu dasu ba, kawai tura musu link din zakayi su kuma su cike. Kamar a kwana kwanan nan da mutane da yawa suka cike training na NITDA Blockchain Technology dinnan anyi amfani da google form ne wajen tattara information din applicants wato wanda sukayi applying, idan zaku tuna ai duk wanda ya cike wannan application din wani link ya shiga ya saka sunansa da email dinsa da sauran bayansa to wannan shine google form.

Sannan idan kana yin training a online ko wani abinda ya shafi jarabawa ko attendance to zaka iya amfani da google form domin ka saita jarabawar da kakeson kayiwa dalibanka ka tura musu link su kuma suyi jarabawar ta cikin wayarsu ko computer ba tare da sunshiga aji ba da sauransu. Matakan da ake bi domin amfani da googe form ko saita shi sune; na farko kyauta ne sannan dole sai kana da email sai kuma waya ko computer duk sunayi.

Zuwa anjima idan Allah ya kaimu zan dora video din yadda ake saita shi kanshi google form din ma domin kugani ta yadda zaku iya saita shi nagode

Sadiq Abdullahi
Nit Digital Services
#Learnwithsadiq

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Click Here To Enjoy Free Browsing