Tech News

Google My Business Tare Da Yadda Ake Saita Shi Don Bunqasa Kasuwancinku

A matsayinka na wanda kake gudarnar da sana’a ko kana da kamfani har kullum burinka shine ka fadada kasuwancinka ko kamfaninka musamman ma yanzu ta hanyar zamanantar dashi. Dalilin haka kamfanin google suka samar da shafin Google My Business, shafi ne da zakaje kayiwa sana’ar ka register ko kamfaninka register KYAUTA ba tare da ka biya ko sisi ba, abinda kawai kake buqata shine email.

Google my business shafi ne da yake taimaka maka wajen kawo maka customers abinda nake nufi da hakan shine idan kayi register da Google My Business zaka saka sunan sana’arka ko shagon ka, sannan zaka saka duk wasu information da ya danganci sana’ar ka misali lambar waya, lokacin aiki, address da sauransu ta yadda mutane zasu tuntube ka.

To duk lokacin da mutum yaji yana son siyan abu ko yanason wani service wata kila kuma baisan inda zaije ya samu ba, yawancin mutane suna shiga google suyi searching misali mutun ne yayi tafiya zuwa wani garin kuma yana jin yunwa baisan garin ba baisan inda zaije ya siya abinci ba, to kawae sai ya shiga browser dinsa ya saka “restaurant near me” a lokacin da ya saka google zasuyi amfani da algorithm nasu su nuna masa restaurant din da yake kusa dashi tare da lambar wayar restaurant din, lokacin aikin su har ma da hoton shagon, amma fa idan har su masu restaurant din sunyi register da Google My Business,

Don haka kuma mai kuke jira domin bunkasa kasuwancin ku ko sana’arku ta hanyar bude profile da Google My Business, bari na ajiye link wanda zaku shiga kuyi register kyauta
https://www.google.com/intl/en_ng/business/
Kuna shiga zaku ga gun da aka saka “MANAGE NOW” sai ku dannan ku fara cike duk wasu bayanai. Ina fatan wannan zai taimaka sosai Nagode

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Click Here To Enjoy Free Browsing