Digital Marketing Tips

Ko Kun San Amfani Da Albarkatun Dake Kafar Sada Zumunta Da Internet Kuwa?

Mutanen mu da dama sun dauka cewa hawa Social Media ayi comment ayi sharing hotuna, videos, ko kuma comments na batanci ko cin zarafi a post na mutane, shikenan amfanin Social Media a wurin wasu da dama, wasu kuma basa comment ko posting, kawai yan leken asiri ne.

KU ZO KUJI
Amfani da kafar Sada Zumunta yadda ya kamata, zai iya kaika wani matsayin da baka taba yin tunani ba a rayuwa, saboda idan kayi amfani da ita ta yadda ya dace shine zaka amfana sosai kuma ka amfanar da al’umma ga baki daya.

SHAWARA
Idan har kana amfani da Kafar Sada Zumunta bata hanyar data dace ba, to wannan shawara shine zan baiwa al’ummar mu, shin kuna da sana’a? ko kuma kuna da wani abu da kuke son koya? Ko kuma abun da kuke kan koya? Me zai hana ku dauki business dinku zuwa wani mataki a cikin wannan sabuwar shekarar da muka shiga, idan ma skills ne ku tabbata kun zaba wanda zaku maida hankali a kan shi.

ABUN DA NAKE NUFI
Idan kuna da sana’a kuma bakwa posting abubuwan business naku a Social Media to lallai yanzun shine lokacin daya dace ku fara tallata kasuwancin, idan kuma kuna koya, lallai ya kamata ku zage damtse wajen maida hankali wurin koyar sa’ar ku musamman Digital Skills, sabo da shine zai baku daman tallata hajar ku ga mutane wadanda baku ma san inda suke ba. Domin haka, ku bude Facebook page, Instagram and Tiktok account domin tallata hajar ku.
Akwai babban Alheri a Kafar Internet, ku sa a cikin ran ku cewa lallai zaku habbaka sana’ar ku ko kuma ku koya sabon Skills da zai dinga saman maku da kudin shiga.

DAGA KARSHE
Duk abun da kuke karku saka kudi a matsayin abun farko da zaku samu, ku saka cewa kuna son koyon wannan abu ko kuma kuna kokarin kawo abun da mutane zasu amfana, kuma ku jajirce, lallai idan kuka jajirce wurin habbaka al’amurorin ku, Allah zai taimakeku a cikin Lamarin ku.

Allah yasa mu dace.
Daga: Muhammad Abdullahi (Facebook)
1st January, 2023

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Click Here To Enjoy Free Browsing