How To
Trending

Masu Tafiya Suna Danna Waya Ku Kula Da Wannan

A lokuta da dama da yawan mu mukanyi amfani da wayoyin mu a lokacin da muke tafiyar kafa, wanda hakan yake saka hankalin mu ya dauke,  wanda a irin wannan lokacin akan samu matsaloli kamar tuntu6e, karo ko kuma a samu akasi mutum ya fada rami da sauran su.
Toh wannan wani setting ne da idan muka saita shi zai taimaka mana wajen tunasar damu cewa  mu kula da amfani da waya, a lokutan da muke tafiya wanda wannan tunasarwa zata sa ka dawo cikin hankalin ka, har ka lura da abubuwan da suke gaban ka domin gujewa fadawa daya daga cikin abubuwan da muka lissafo a baya.
Yanda zaka saita abunnan  a cikin wayarka kuwa shine:
  • Da farko za kaje SETTING a wayar ka
  • Sai ka shiga DIGITAL WELLBEING
  • Sai kaje can kasa, zakaga inda aka rubuta HEADS UP saika shige shi
  • Daga sama zakaga abun a kashewato switch saika kunna shi

Shikenan, yanzu a duk lokacin da kake tafiyar kafa kuma kana amfani da waya a lokacin zai dinga tunasar da kai domin ka kula don kar wani abu ya sameka. Zaku iya duba hotunan kasa domin ganin yadda ake saitawa cikin sauki. Sai dai a kula: Ba laillai ko wacce waya ce take zuwa da shi ba

Rubutu Daga: Haruna Abubakar Liye

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Click Here To Enjoy Free Browsing