Mu Koyi Computer
Trending

Mu Koyi Computer Part 1

Mecece Computer Tare Da Abubawan Da Suka Bayar Da Computer?

Computer wata naura ce da ake amfani da ita wajen ajiye sakonni, turawa da kuma fitar dasu, computer ta zama jigo a rayuwar mu da muke amfani da ita wajen ayyukan mu na yau da kullum kamar a  kasuwanci, ma’aikatun gomnati, asibitoci, makarantu da dai sauransu, Duk wata naúra da ta ke sarrafa bayanai tare da adana da kuma fitar dashi ana kiranta da computer

ABUBUWAN DA SUKA BADA COMPUTER

Akwai abubuwan da suka hadu suka bada computer wato Software da Hardware wadannan su suka hadu suka bada abinda ake kira computer.

  • SOFTWARE: Wani bangare ne a cikin computer wanda ba’a iya gani da Ido ko a iya tabawa, software na bawa computer umarnin duk wani abinda zatayi, kama daga kunnata, tura sako a computer, ajiyewa, da dai sauransu duk aikin software ne.

IRE-IREN SOFTWARE

  1. SYSTEM SOFTWARE: Itace rai na computer da take aiki tare da hardware, ba tareda system software ba computer ba zata samu damar yin wani aiki ba, idan har babu system software, computer zata zama kamar gangar jikine babu rai. Daga cikin system software sun hada da:
  • OPERATING SYSTEM: Wani bangare ne a cikin system software da manyan companies suka kirkira wajen taimakawa computer yin aiki.

IRE-IREN OPERATING SYSTEM

  • Windows: Operating system ne da kamfanin Microsoft suka kirkira domin sakawa computer, mafi yawan computers suna amfani da Windows ne domin yafi shahara da saukin aiki. Windows ya kasu  kala-kala daga cikin wanda akafi sani akwai: Windows 7, Windows 8, Windows 10 da Windows 11

 

Insha Allah anan zamu tsaya a yau  a cikin darasin nan namu na mu koyi computer, kar ku manta ku kasance tare da ni a ko da yaushe domin cigaban wannan darasin namu. Sannan ga masu buqatar ganin wanin darasin tare da bayanin computer din zaku iya kallon videon da ke kasa nagode sosai

 

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Click Here To Enjoy Free Browsing