Tech News
Trending

NITDA 3MTT Program Me Ya Kamata Kusani?

Cikin wannan post din a yau zan iyar da bayanin sauran courses 3 da suka rage, cikin 12 courses din da NITDA ta ce zata koyar ga 3Million Nigerians. Courses din da zan yi bayani a yau sune:

10. Quality Assurance
Quality Assurance skills ne da yake tabbatar da bin ka’ida wurin kirkirar abunda company zaiyi, ko kuma service din da company zai yiwa mutane, tareda ba da shawara ko tabbatar da cewa company yabi duk wata ka ida da ya kamata abi wurin samar da ingantaccen Product ko Service ga Customers, sannan masu Quality Assurance skills zasu tabbatar da suma Customers ko Clients sun samu gamsuwa tareda karbar product ko service din da company zai basu ta hanya ingantatta da kuma gamsuwa. Quality Assurance Technician or Assistants suna cikin profession din da duk wata ma’aikata ko masana’anta to tana da bukatar su a tare da ita.

Quality Assurance ilimi ne da dayawa mutanen mu basu san shi ba, amma duk wata babbar ma’aikata ko industry to akwai wadannan professionals din a wurin.
Misalin yadda aikin Quality Assurance yake:
Company ne zai kirkiri Software domin taimakawa mutane su dinga saving na kudin kasuwancinsu.
Quality Assurance Technician aikinsa shine, ya tabbatar da cewa Software din anyi ta bisa ka’ida, bata sabawa kowace doka ba ta Gwamnati ko ta Company din, sannan ya tabbatar Software din zata amfanar da targeted clients din, sannan kuma zasu iya amfani da ita ba tareda sun sha wahala ba ko sun karya wata doka ba.
Anan Quality Assurance Technician har survey zai iya yi, sannan yayi conducting analysis, kuma ya bada report akan findings nashi game da Software din, don gujewa faruwar wani abu.
Da yawa masu wannan skill na Quality Assurance suke bada shawarar ayi Product kaza ko ayi rendering services kaza a Company, ko kuma ayi improving na product kaza saboda sunyi research sun gano, product din is not up to standard, ko kuma mutane na korafin kaza da kaza.
Ga masu son irin wannan ilimin, sai su yi applying na Quality Assurance, bansani ba a Nigeria idan ana Quality Management as a course a Jami’a.

11. Cloud Computing
Cloud Computing agurguje kamar kace digital computer ne, ma’ana wannan Computer da muke amfani da ita muna aiki, muna saving files namu da sauran data aciki, to muna iya muyi moving kome namu a Cloud ta yadda computer dinmu ce kawai a gaban mu, amma duka files na mu suna a Cloud, don haka ko an sace computer din, ko ina muke a duniya, muna iya accessing files namu muyi duk abunda muke so, wannan shi ake kira da Cloud Computing.
Ci gabane yanzu da yazo ta yadda, koda Company zai yi gobara, ko ayi sata acikinsa, babu data ko guda da zata bace, ko za’ayi hasara, saboda duka files da kome na Company din anyi storing nasu a Cloud.
Akwai manyan companies guda 3 da sune Cloud Computing service providers, kamar su Amazon Web Services (AWS), Google Cloud Platform (GCP), and Microsoft Azure, dukansu zaka iya sayen space a wurinsu, domin su aje maka kome naka a wurin, ta yadda computer dinka dakake aiki da ita, tamkar hoto ce, amma asalin files naka da kome ba a cikinta suke ba.

So akwai Cloud Computing Engineers, Assitance, da sauransu, bansan exact me NITDA zata koyar ba, amma samun ilimin Cloud Computing yana da amfani sosai, musamman yadda mutane suke komawa a can, saboda saukinsa da kuma romon da ake dashi.
Because, idan kana amfani da Cloud Computing, babu ka ba hiring Cyber Security Expert ko IT Specialist a Company naka, duka wadannan services din, su Cloud Computing Service Providers din su zasu maka rendering nasu, kuma su zasu yi protecting na Data dinka da kome naka.
Masu son wannan ilimin sai suyi applying.

12. Dev Ops
Development (dev) Operations (ops) skills ne a IT industry wanda ake amfani dashi domin ayi designing hanyar da za’abi domin kirkirar wani abu, tun daga farko har zuwa karshensa.
Wannan ilimin anfi amfani da shi wurin Software Development, shi yasa wasu suna kiran sa da Software Development Operations (DevOps).
A wannan ilimin, ana tsara yadda za’ayi Software tun daga farko har karshe, ma’ana anraba aikin ne a Stages guda biyu, stage na DEVELOPMENT da kuma stage na OPERATIONS.
A Stage na DEVELOPMENT anayin:
– Planning
– Coding
– Building
– Testing
A Stage na OPERATION shikuma za’ayi:
– Releasing
– Deploying
– Operating
– Monitoring
Mai son wannan ilimin sai ya yi applying nasa.
A karshe, wannan shine karshen bayanin da zanyi akan wadannan courses din guda 12 da NITDA zata koyar da mutune har 3Million.
Ina fatar wannan zai taimakawa wadanda sukayi applying already, da su san abunda zasu koya, sannan su fara shiri kafin program din ya fara.
Allah kasa mudace baki daya, ya amfanar da al’ummar mu da wannan ilimi da zaa koyar.

Copyright by: Ahmad Aminu Ahmad,
+2347066309565
ahmadaminuahmad@gmail.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Click Here To Enjoy Free Browsing