Tech News
Trending

Sabbin Update Da Akayi A Social Media 2022

1) Whatsapp
– Zaka iya saita disappering message wato idan kana chat da mutum zaka iya saita messages dinka dashi su goge bayan wasu awanni ko kwanaki.
-Profile Picture Privacy; yanzu zaka iya saita iya wanda kakeso su kalli Profile picture dinka wato D.p ma’ana zaka iya boye shi idan bakason kowa ya gani a whatsapp.
-Anyi adding yaren hausa a whatsapp masu buqatar amfani da yaren hausa yanzu a cikin whatsapp an bayar da dama.
-Adding mutane sama da 500 a cikin groups ba kamar a baya ba da iya mutane 250 ake adding.

2) Facebook;
-An bayar da damar copy and paste ga masu amfani da facebook lite sakamakon a baya ba ayi.
-An karawa facebook security yanzu kowacce lambar waya ko email sau daya tak za’a bude account da ita sabanin a baya da ake multiple account.
-An kara gyara tsarin payment na sponsored ads ga business pages.

3) Telegram;
-Yanzu telegram sun bayar da dama uploading file mai nauyi har kusan 4gb.
-An fito da tsarin subscribtion ga masu amfani da telegram yanzu zaka iya zama premium users zaka ringa yin subscribtion duk wata (ba dole sai kayi ba) idan kayi zaka samu tambarin verified user kuma channel dinka zaka iya saka unlimited members.
-An tanadar da voice to text a telegram idan ka zama premium user zaka iya zaka iya mayar da voice ya koma rubutu a telegram.

4) Youtube;
-An kawo tsarin short wato ga youtube creators suna posting content da bai wuce minti 1 ba domin channel dinka ta zama active agun Subscribers dinka tare da kuma kara jawo maka wasu subscribers din.
-Copyright claim check: shima tsari ne da youtube suka fito dashi domin youtubers idan zasuyi posting content, youtube zasu tabbatar content din bashi da matsala ko kuma bana wani ne ka dauko zakayi amfani dashi ba domin gudun copyright.

5) Twitter;
-An kirkiri wani abu da ake kira da space wato wanda zai bawa ma’abota twitter dama su tattauna live ta audio ba tare da sun sha wahalar yin rubutu ba.

6) Tiktok;
-Yanzu tiktok sun fito da update din da zaka iya posting video din da ya kai har tsawon minti 5
-Sannan sun fito da tsarin da ake cewa gift wanda zai baka damar samun kudi idan followers dinka sun kalli video dinka zasu iya baka kyauta wanda idan ka tara tiktok zasu baka kudinka.
A matsayinku na masu amfani da social media wannan update ku kaci karo dashi a shafukan sada zumunta da kuke amfani dasu wanda baku ganeba ko kuma banyi bayanin shi ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Click Here To Enjoy Free Browsing