Digital Marketing Tips
Trending

Shawarwari Idan Kuna Son Fara Social Media Marketing

Bincike ya nuna a kullum masu amfani da kafafen sada zumunta Karuwa suke, don haka kullum cigaba yana zuwa ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta domin yin kasuwanci, koyarwa da sauransu, ba wai kullum muna hawa social media ba tare da mun koyi wani abu wanda zai amfane mu ba duk an daina wannan rayuwar a social media yanzu.

Zan yi takaitaccen bayanin wasu hanyoyi da in har dai kunason kuna amfanuwa da social media handles dinku domin kasuwancin zamani, hanyoyin kuwa sune;
1) Ilimi: Tun daga farko yana da kyau kafin ku fara kasuwancin social media yana da kyau a nemi ilimin abun akwai shafuka da manhajoji da makarantu da suke online wanda ake koyan ilimin kasuwancin zamani wasu kyauta ne ma
.
2) Samun NICHE; abinda ake nufi da niche shine fannin kwarewa, yawanci abinda yake damun wasu mutanen namu idan suna sana’a ko kuma kasuwanci yanar gizo shine basu san niche dinsu ba, ma’ana shine ka samu gun da kafin kwarewa sai ka rike domin kayi amfani dashi misalin irin wanne shine wasu zakuga bloggers ne wasu kuma youtubers, wasu digital marketers, wasu graphic designers wasu kuma programmers da sauransu wannan duka categories ne amma a cikin kowanne category ana zabar niche a ciki, misali idan muka dauki youtubers wasu yawanci zakuga akwai youtube channels din kawai video din wasannin suke sakaw, wasu tutorials, wasu kuma labarai kadai, to wannan shine niche dinsu baza ku taba gani sun saka video din wani abun ba (zan samu lokaci nan gaba nayi cikakken bayani akan shi kanshi niche domin samun fahimta sosai)

3) Samun kafar sada zumunta wadda kafi so: dole ka duba kaga wacce kafar sada zumuta zakayi amfani da ita domin ta zaman maka hanyar mu’amala da mutanenka zaka iya amfani da kowanne irinsu facebook, instagram, whatsapp da sauransu amma ka zabi guda daya ko biyu wanda kasan zaka ringa amfani da ita sosai kuma kana bada lokaci don kada hankalinka ya rabu sosai.

5) Tsara social media timetable; Yana da kyau ka tsara social media timetable wacce zata ringa baka damar sanin lokacin da zaka ringa yin posting kuma kowacce rana da abinda zaka ringa yi, akalla a kowacce rana da adadin post din da zakayi saboda yawanci masu bibiyar shafukanka ba lokacin ka kadai suke dashi ba su na bukatar lokacin su domin yin wani abun nasu a cikin rayuwarsu don haka audience dinka basu fiya son ka cika yin post ba da yawa a lokaci daya, hakan yana rikita su a kalla idan kayi posting sai ka bada interval kamar na awa 1 zuwa 2 sai ka kara wani wannan zai taimaka sosai

6) Hakuri da jajircewa: Dole baza ka fara ba kace a lokaci daya zaka samu nasara dole sai da hakuri da jajircewa sosai sai kayi hakuri kana aiki sosai tare da addu’a domin watarana zaka samu nasara.
Wadannan sune hanyoyin da idan har kukabi domin fara kasuwancin zamani ina fatan insha Allah zaku samu nasara, a hankali zan ringa saka muhimman abubuwan da suka shafi social media marketing da sauransu

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Click Here To Enjoy Free Browsing