Tech News
Trending

Shin Kun San Menene Affiliate Marketing

Affiliate Marketing wani salo ne na kasuwanci wanda kamfanunuwa suke bama mutane tallar kayan su, idan sun sayar su biya su kamasho. Wasu kamfanunuwan kuma, suna tafiyar da nasu tsarin Affiliate Marketing dinne dai-dai da irin tsarin kasuwancin da sukeyi. Misali idan kamfanin aikin gina website sukeyi, kawai abinda suke bukata shine ka kawo masu wanda zai basu aiki kai kuma su biya ka kudin kamashon ka.
Kamfani masu yin Affiliate Marketing da yawan lokaci idan mutum yayi Register dasu, wasu suna bada kalmomin sirri (codes) ga masu tallar kayansu wanda duk wanda ka kawo, yayi amfani da wannan code ɗin naka to zaka samu yan sulallan ka. Wasu kuma suna bada links ne da banners domin talla musamman a shafukan yanar gizo.
Kamfani suna biyan yan kamashon sune ta hanyar percentage. Misali kamar kamfanin Amazon, duk abinda ka sayar kana da 10%. Idan ka sayar da abun ₦100,000 kai kana da ₦10,000. To ka ƙaddara ka sayar da abubuwa 30 a wanda daya wadanda suka kawo maka kamashon ₦10,000 kaga kana da ribar ₦300,000 kenan.
Wadanda suka mayar da hankali sosai akan harkar Affiliate Marketing suna samun kuɗi sosai masu tarin yawa. Saboda sunfi da yawan ma’aikatan gwamnati ko wasu kamfanin samun kuɗi. Nasan zakuyi mamaki idan akace akwai Affiliate marketer dake samun sama da ₦700,000 a wata. To haka abun yake kam ana samu sosai.
Kadan daga cikin websites da zaku iya shiga domin yin Registration na Affiliate Marketing akwai:
Akwai wasu masu yawa sosai wadannan kadan ne muka dan tsakuro maku.
A wajen yin Registration musamman a Jumia, akwai matakai da mai Register zai iya cikewa.
– Micro influencer: Wanda zai cike wannan, ana bukatar ya samu 5000-100,000 followers a social media handle ɗinsa. Idan ka gama Registration yina daukar sati daya zuwa hudu kafin su gama reviewing.
– Mega Influencer: 100,000 followers zuwa sama.
– Business/Individual agent: shi wannan na kowa da kowa ne koda mutum baya da followers zai iya applying.
Credit: Abubakar Sani Dan Bahaushe  (Fanthecher Technologies)
Source: Facebook Handle of Abubakar Sani DanBahaushe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Click Here To Enjoy Free Browsing