How To
Trending

Shin Menene YouTube Handles

A kwanan nan kamfanin Youtube suna turawa duk wasu masu amfani da manhajar wato Youtubers sakonnin ta email, da nufin cewa zasu kawo wani tsari ko feature mai suna Youtube handles.
Handle wani tsari ne da YouTube suka kawo wanda zai fara aiki a cikin watan nan, amfanin sa shine a yanzu kowanne Youtuber indai har yana da channel to dole sai yaje ya saita handle, a takaice dai handle kamar username ne da muke amfani dasu a social media irin su Instagram, twitter, Facebook da tiktok.
Abin nufi shine yanzu kowacce channel zaka saka mata handle dinta wato username din da kakeso, idan har kasaka to babu wani wanda zai saka irin wannan username din; hakan na nufin kai kadai ne mai wannan username din.
Mu dauki misali a instagram, idan ka bude instagram profile idan ka zabi username babu wani wanda zai sake saka irin wannan username din dole sai dai mutum ya kara da wasu lambobin ko kuma wasu special characters din, misali ka bude instagram da suna ABC idan wani yazo bude instagram yanason saka username dinshi shima ABC to hakan bazai yi ba sai dai instagram suce sai yayi adding number ko underscore sai dai yayi amfani da kamar ABC1 ko ABC_. wani karin misalin shine kamar email; shima idan kana da email babu wanda zai iya bude wani email din da irin wannan sunan da kayi amfani dashi, dole sai dai ya kara lambobi ko wani abun, to haka su ma yanzu YOUTUBE suka fito da tsarin su kowacce channel yanzu zatayi amfani da username dinta na kanta.
Sai dai tun a baya idan mutum yana amfani da Youtube akwai personalised ko custom URL da mutum yake saitawa channel dinsa zakuga wasu channel din suna da custom URL dinsu irn haka www.youtube.com/c/ChannelName irin wannan shine custom url da mutum yake saitawa. To idan har ka saita custom url dinka, wannan sabon tsarin na Youtube handles zaiyi amfani da custom Url dinka a matsayin handle dinka,
Idan kuma kai dama sabon Youtuber ne baka saita custom url dinka ba, alfarmar wannan sabon feature din Youtube sun baka dama ka saita handle dinka tare da custom url din channel dinka.
Akwai wani class dana tabayi akan Youtube tun daga matakin farko har karshe duk wanda sukayi class din nan na tabbata yanzu zasu iya shiga youtube su saita handles dinsu
A Kula: Handle ba wai canja sunan channel dinku bane kawai username ne na channel. Nagode da fatan an ilimantu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Click Here To Enjoy Free Browsing