How To

Wanene Digital Marketer

Shin Wanene Digital Marketer? Tambayar Dana Samu Daga Wani Bawan Allah.

A wannan zamanin yanzu zamuga mutane da yawa na son zama digital marketers amma sunason sanin wanene ma digital marketer tare da kuma aikinsa ma.

To da farko dai digital marketer mutum ne kamar kowa sai dai shi yana taimakawa masu sana’oi ko yan kasuwa wajen cigaban kasuwancin su tare da samo masu customers, followers, ko kuma taimaka musu wajen siyar da kayansu ta hanyar amfani da kafofin sada zumunta na zamani wato social media platforms irinsu Facebook, Instagram, Tiktok da sauransu

Kafin ka zama digital marketer dole ne kana buqatar kasan ilimin social media ko yaya ne sannan sai kana da waya ko kuma computer wanda sune kayan aikinka domin dasu ne zaka ringa yin aiki wajen posting tare da managing aikin da mutane suka baka.

Idan muka duba yawancin pages na wasu ‘yan kasuwan, yan films, yan siyasa da sauransu da yawansu social media managers ne ke yi posting tare da kula da shafukansu. Digital marketer ba dole sai kana managing page ba indai kana da skill wanda kake amfani dashi kuma zai taimaka wajen bunkasa kasuwanci to kaima digital maketer ne, daga cikin ire-iren digital marketers sun hada da;

Affiliate Marketers
Graphic Designers
Social Media Managers
Web Designers
Video Editors
Da sauransu Da Yawa.

Zama Digital marketer sana’a ce wanda zaka dogara da kanka ko da kana wata sana’ar zaka iya zama digital marketer lokaci kawai zaka samu da iya wayarka ko computer dinka zasu zamar maka hanyar samun kudi a maimakon bata lokacinka kana shafe awanni kana wani abin wanda bazai amfanar da kai ba a online, da yawa akwai masu business din da sunanan kullum suna neman digital marketers kuma a shirye suke da su biyasu ko nawa ne indai zakai musu aiki kuma sun tabbatar da aikinka mai kyau ne kuma babu cutarwa a ciki .

Shawara ta anan shine idan har kanason zama digital marketer to yana da kyau ka nemi ilimin digital skills ko da guda daya ne wanda kaga ya dace ka koya kuma zaka mayar da hankali ka kware akai, ba wai kayi sau daya sau biyu ka ajiye ba, da iya digtal skill dinka zaka iya samun 100k zuwa sama a cikin wata daya.

Kafin nan bari nayi wata tambaya, shin ka shirya zama digital makerter, sannan wanne skill kakeson ka kware akai tare da kuma amfanin da kake tunanin zai yi maka?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Click Here To Enjoy Free Browsing