How To
Trending

Yadda Ake Saka Windows Operating System A Cikin Computer

Lokuta da yawa masu amfani da computer suna son su canjawa computers din su operating system zuwa latest wanda ake yayi misali daga windows 7 zuwa windows 8 ko kuma windows 8 zuwa 10 ko zuwa windows 11, a wasu lokutan kuma wasu sun siyo computer tazo da 32 bit operating system kuma ba kowanne software ne zai yi installing a ciki ba, dole mutum yana buqata yayi upgrading zuwa 64 bit, don haka dole mutum yana buqatan a canja masa operating system wato window.

Kafin ku canjawa computer dinku windows ga hanyoyin da zaku bi amma sai kun kula sosai;
– Ku nemo window din da kukeson zaku sakawa computer din taku a matsayin .ISO format. DANNA NAN DOMIN DOWNLOADING WINDOWS 10 – Ku samu flash wanda a kalla yana da space yakai 8GB domin dashi zakuyi amfani.
-Dole ku mayar da flash din naku bootable domin saka windows din akan flash din, hanyar da zaku mayar da flash bootable akwai softwares da ake amfani dasu da yawa amma ni nafi amfani da power iso da kuma rufus (basu da nauyin daukowa.) DANNA NAN DOMIN DAUKO POWER ISO – Idan zaku mayar da flash dinku bootable file sai kun goge komai a cikin flash din.
– Abu nagaba shine sai ku kashe computer din da zaku saka mata window din sai ku saka flash din da kuka mayar bootable a jikin computer din sai ku kunna computer din tana kawo haske zakuyi sauri ku danna ESC a cikin keyboard dinku zata nuna muku boot menu option wata boot menu option dinta F2 ne wata kuma F10, wata F12 wata ma F9 ya danganta da computer din.
– idan kuka shiga boot menu na computer din zakuga sunan flash dinku sai ku zaba shi.

So daga nan sai ku bi instructions din da zaku gani, zai baku damar selecting kalar windows din da kukeso misali idan windows 10 ne akwai windows 10 pro, 10 home, 10 education, da sauransu , Sai ku zabi akan local disk din da zakuyi installing windows din.

Zaku ya duba videos din dake kasa domin ku ga yadda ake sakawa tare da mayar da flash cikin sauki

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Click Here To Enjoy Free Browsing